Friday, 16 September 2016

ZEENATU 8

*ZEENATU by Queen meemi page8*

♠.         ♠.         ♠.           ♠.           ♠.           ♠
♠.              ♠.          ♠
                *®NWA*
*dedicated to lubie maitafsir & Benazir*
     *[9 Sep 2016]*

********
Zee tsaye a Gaban Allo ajin yayi tsit Ana jira aji ta fara karatun haddar da aka basu malam haruna dake tsaye ganin Zee Tai shiru yace "zeenatu ke nake saurare" tsuru -tsuru Tai da idanuwa take ya Nuna Munay da taxo Tai nata karatun Cikin nutuswa ta karanto dai-dai iya Inda akaa basu haddar haka ya umarceta dataje ta zauna ya kirawo Aneesa itama tayi ta zauna nan ya had'e rai ya juya gun Zee yace " wato duk abokan surutun naki sun iya haddar banda ke ko? me ya hanaki to"?. Shiru Tai ya daaka Mata tsawa ,jiki na rawa tace" ya sayyadi wallhi k'auye mukaje biki shiisa banyi haddar ba Amma na iya rabi " "ay dama zeena bakya hadda to wallhi kinsan Allah,idon baki haddar nan ba sekin D'an D'ana " ya sayyadi ta fad'a kallonta Yai "meye"? Dama cewa nai zan biya da qur'anin nan ya mika Mata aya biyu ta karanta Tai shiru ya d'ago ya" Naga kink'i k'arasawa nan ta kai qur' anin dai-dai idon ta ya" sayyadi bana ganin rubutun ne haka ta mutsits-tsike idonta ta kuma k'urawa qur anin Ido ,"wayyyo Allah na wai meya faru da idon nawa ne"? Hata kuma maimai ta ayoyin  bayan haka ta kuma tsayawa dariya malam haruna yasa nan 'yan class ma suka tuntsire da dariya.

*******
Haka tabisu da Ido Tai k'wafa ,"ya sayyadi na gama" ta sunkwi dakai ,had'e rai yayi ai" sekin k'arasa kunya ce ta isheta ta kai wajen mintuna ahaka ganin zata b'ata musu lokacin yasa ya karb'e qur'anin yace ta matso kamar an dasa ta.

*******
"Ba dake nake magana ba" bulala ya d'auko Yai Mata k'warara biyar ya K'ara Mata page d'aya "kuka take ahankali tana matse Ido munay ta sunkuya tana dariya haka malam haruna ya cigaba da karatunsa ita kam se kalle-kallen 'yan class en take taga Wanda yai Mata dariya ta rubuta Shi alist can ta gano ummi bogaza sunan Wata aclass en nasu dariya Zee tasa ganin bogaza da Tai na dariya haka malam haruna ya gama ya fice k'irrrr aka kad'a da sauri taje wani lungu ta tsaya ganin bogaza yasa tazo ta rik'eta "wa kikewa dariya don na kasa hadda " wallah ni ban miki dariya ba jikin ta se b'ari yake don dama tsoron Zee take d'uuu 'yan makaranta sukazo wucewa nan suka taru Wata kubra tace" ummi wallahi kima Zee duka kalleki ba jibgegiya  duk ajinmu ba Wanda ya kaiki k'iba Amma ki zauna jikinki na kar- karwa kan Zee".

ganin hakan yasa Zee ta cafko ummi bogaza ta kai Mata duka dambe suka fara ummi bogaza ta d'aga Zee takai kass I'donta ya rufe sai dukan Zee take zo kuga idon Zee ya raina fata se Hawaye take cikin k'arfin hali ta gantsarawa bogaza cizo nan fad'an ya kuma rikicewa sai da wani mutum yazo wucewa ya rabasu kowa ya kama gabansa.

********
duk dukan nan da tasha bai sa ta hak'ura ba, haka tai ta falfalar gudu ga k'afarta na Mata zafii dukan da bogaza Tai Mata ,sai da ta kamo su munay har sun kusa Zuwa gida ta cakumo munay, munay tace" me nai miki"? Ai" kema kin san me ki kai mun dariyar da kikai mun kin d'auka zata tafi a banza ne"? Haka ta gasawa munay rak'washi take suka hautsine  Aneeaa na rabasu lokacin 6 dai-dai dadyn Zee zai tafi masallaci ya ganota, dak'yar ya rabasu yace "yanzu zeena yauma fad'an naki kika tsaya"? ga maminki can na nemanki " ya kalli munay daketa gurshek'en kuka ya bata hak'uri ya tambayeta meya had'asu nan ta rattaba mai cikin Jimami ya kalle Zee "yanzu kan hakan kika yaga Mata hijab har Abada ke baki da hak'uri wace irin zuciya gareki ne ehe"? naira hamsin ya d'auko ya bawa munay yace  taje a d'inke Mata.
haka ya juya ya kalli Zee ya nuna Mata hanyar gida,haka ta tafi duk fuska a karce saboda fad'a ga Shi tana d'ingishi.

*By*
   *Queen meemi* .
*Meemqueen blogspot.com* .

No comments:

Post a Comment