. *ZEENATU by Queen meemi page 9*
♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠
♠. ♠. ♠
*®NWA*
*dedicated to Lubie nd bena*
*[17sep2016]*
Haka taje gida tana d'ingishi mum dake kitchen tana kwashe tuwo ta ganta tace" Aa Zee meya faru da k'afar ne"?sukwi dakai tai bata ce komi ta shiga d'aki mum ta girgiza kai tabbas tasan fad'an nata ta janyo ,fitowa Tai ta d'ebo ruwa a buta ta fara Alwala dede zuba ruwan da Tai a fuska ta k'wala k'ara mum ta fito " ke mene" ?ganin fuskarta duk akarce yasa mum ta sa dariya "ai maganinta kema. Ayi mutum bai da Aiki se fushi da fada tunda Naga fuskarki nasan kinyi fad'a,da k'yer Tai Alwalar taje Tai sallah .
*8 :pm*
******
duk suna zaune Ana ta kallo Zee ta had'e rai sai k'wafa take,tsam ta tashi ta ta shiga d'aki ta d'au qur'aninta tana hadda "mum wai me akaiwa Zee ne"? cewar sadiq mum tace" kasan Halin yayar taka kutsuwa ce" haka suka kwanta ba wanda ta cewa k'ala.
*7:am*
da safe kuwa kowa ya tashi Zee ta kasa tashi.
Sai da mum ta shiga d'akin ta tadda ta tana kuka sosai "wayyo mum k'afata na kasa tashi" taci gaba da kuka "muga kafar " mum ta d'aga k'afar taga ta kumbura daga gefe "Ashsha! garin yaya haka Zee"? sadiq dake k'ok'arin shiga d'akin yace "mum inaga fad'an da sukai ne da ita da wasu kawayenta ,domin Naga suna ta dambe Allah mum Dan bakiga wadda suke fad'an da itaba gandamemiya ".
dariya mum tasa ah" da walakin ai dama tin jiya na gano
Ai ga Shi nan Wata abanza ta jibgeki ke zeena ki Dena neman fad'a ayi mutum baya yafiya wallhi ke zaki sha wahala banza ahofi " zumb'ura baki Tai "mum dariya fa suke mun "
d'aga ta mum tayi k'ara ta saki sadiq sai dariya yake "Allah mum inna warke sai sadiq ya sani ".
Mum tace " Allah de ya Sawwak'e miki Zee ".
Da k'yar ta tashi ta kaita falo ta ebo ruwan zafi tana gasa Mata ,lokacin dadyn su ya fito zai kai su sadiq da sadeey da faty school nan ya tambayi meya faru,take mum taga ya mai.
Dady yace"Ai jiya nan nan na ganota suna fad'a da yaran gidan Alhaji tanko wai sun Mata dariya don takasa hadda"
Mum tace "Ah to Wanda baiji bari ba ai yaji hoho ai gashi nan jikinta ya gaya Mata".
Dady ya fita yace zai dawo da mai gyaran targad'e don da Alama Tai targad'e haka Tai sallah a zaune .
Wajen 12 Dady ya dawo da mai gyaran targad'e kama k'afarta yai ya duba nan ya fara gyarawa tun tana matsae -matse har ta fara ihu mum na rik'eta kuka sosai take.
Bayan ya gama ya bada magani asha fa agun haka ta zauna tana jinya .
Da yamma Dady ya kawo Mata hanta gasashshiya da milk nan Zee ta hau murna haka Tai taiwa su sadiq dangwaliliya .
*7pm*
********
su munay da Aneesa suka zo dubiya Zee sai harare-Harare take Aneesa ta fito da Iv ta mik'awa Zee "gashi na bikin Anty ramla ne ranar Sunday" dariya tasa don Zee akwai son zuwa biki ko ba a gayyace ta ba.
Munay tace" to idan lokacin baki warke ba fa"?
"To 'yar bak'in ciki wlh ko ban warke ba senaje shine first fa da aka fara gayyatana biki"
Shiru sukai san nan suka tafi ,haka Zee Tai ta jinyar fuskrta da k'afarta har Ana I gobe bikin gidan su Aneesa Fes Zee ta mik'e ko Dan washe gari taje biki.....
*© Queen meemi*
*Meemiqueen.blogspot.com*
No comments:
Post a Comment