Saturday, 17 September 2016

ZEENATU 10

. *ZEENATU by Queen meemi page10*

♠.             ♠.           ♠.       ♠.              ♠.            ♠
♠.                ♠.              ♠
               *®NWA*
*dedicated to Lubie & bena*
     *[18 Sep,2016]*

Tun sassafe Zee ke duba kalar Kayan da zata sa ko wanne se taje ta duba mirrow ta ga yanayin zamansa a k'alla ta d'auki kaya sun kai kala 5 duk basi Mata ba se ak'arshe ta gano wani kayan ta da Anty bara ta d'in koma Mata Harda mayafinsa ta aje gefe har wani yanga take .

Haka taje ta duba takalman ta ta gano wani me d'an uban tsini Wanda sanda sukaje kano aka sai Mata ,Shi ma ta d'auko ta aje a gefe.
   Mum dake shiga d'akin "oh su Zee gargaji ga ke tun yanzu kike had'a kayan zuwan bikin sekace Wata shaharriyar budurwa " dariya tasa mum" wallahi kwalliya zanci don har powder da lips stick zan sa"                   "haka ai akeso ki nutsu saura kuma kije ki neman fad'an agun biki"
   "Mum ai bazanba "
Bud'e kanta Tai tagan shi a cunkushe nan mum Ta taje Mata tasa ribborm .
  Saboda dad'in za ta biki sai Aiki take yau har dasu wak'e -wak'e lokaci kad'an -kad'an sai ta kalli agogo haka da rana kowa ya kwanta bacci da yake weekend ne amma Banda Zee ta kafawa agogo Ido.

*3:pm*
*******
Zumbur Zee ta mik'e ta shiga wanka so biyu tana sab'a sabulu da gudu ta fito ta shige d'akinsu ta tsane jiki ta mulka mai Abu kad'an sai ta kalli agogo haka ta zira kayan dai-dai sun Mata kyau adai-dai shekarunta d'akin mum ta shiga lokacin tana kan sallaya "mum ki mun kwalliya na kasa kin san ni ban iya ba "
   "To dama wane kwalliya za ki iya aise fad'a" dariya Tai" kai mum ai na Dena "
   To Allah yasa my Zee haka mum ta zizarawa Zee kwalliya tasa Mata kwalli sosai a idon da yake masha Allah Tana da wadatattun idanuwa dara-dara tasa Mata lipstick ta taje Mata gira da yake irin girar nan ce da ita cunkus me yawa bak'a Sega zeee d'au skin inta me kalar choculate ta haskaka.
    Haka ta feshe ta ta perfume sai ga zee Tamkar flower Tai kyau sai kallon mirrow take tana murmushi "mum dama Nima ina da kyau".?
  "Sosaima Zee ai sema kin Dena fad'a kyanki zai dad'a fitowa"  Tsalle ta daka "ai mum na kusa Daina wa" dariya mum Tai to Allah yasa".
    Agogo ta kalla taga 4:15 da gudu ta fita ta sako takalmin ta da wani mayafi shima dai-dai shekarun ta tsayawa Tai "mum na tafi "
   "Zee kar naji kar na gani ".

************
Ahankali Zee ke tafiya don kar ta fad'I har yanga ake dosar gidan su Anee Tai taga motoci birjik K'ara sauri Tai jikin ta na rawa .wasu manyan 'yan Mata ne atsaye ganin yanda Zee ke tafiya yasa suka sa laugh Wata tace " ga yarinyar can se yanga take kuma masha Allah me kyau da ita, harara Zee ta buga musu dai -dai,shiga gidan taga munay.nan suka tsaya .

Zee tace" wai  a ina za ai ne "?munay tace" a wani big house za ai  kusa da gidan Antyn su Anee ke kings gidan tab ya had'u "Zee ta yatsine fuska "to,mu a ina zamu "? munay tace" bakya ganin motoci ai aciki zamu shiga".
   Ganin an fara shiga su zeee suka doshi Wata dalleliyar mota garin sauri Zee ta buge wani bata Sani ba  jiyawa Tai sukai Ido Hud'u da wani matashin saurayi da sauri  Ta k'arasa suka bud'e motar zasu shiga manyan 'yan Matan nan suka tsai dasu.
    "Ku yaran nan ina zaku shiga? kuje ga bus can nan yara ke shiga" zeee ta tab'e baki tace to" dame kuka fimu "Wata tace zan mauje ki kina kwaila kina cusa kai".
"Zee tace malama duk girmanki ba tsoronki zanji ba ta far-fara idon ta
  Dariya suka sa Zee taja hannun munay suka doshi Wata mota waddama tafi d'ayar kyau bud'ewa  sukai suka zaman su .......ku dakace ni plsss.

*©Queen meemi*
*Meemiqueen.blogspot.com*

2 comments: